Ana Damfarar Mutane Da Sunana A Facebook – Aisha Tsamiya

Fitacciyar jarumar Kannywood Aisha Aliyu Muhammad (Tsamiya) ta yi gargaɗin cewa akwai wasu masu amfani da sunan ta a manhajar Facebook su na zambatar mutane.

Jarumar ta ce akwai masu amfani da sunan ta su na tallata kayan da ta ke ɗorawa a shafin ta na Instagram domin damfarar mutane.

Tsamiya, wadda ta yi wannan gargaɗin a wani guntun bidiyo da ta fitar a daren jiya, ta ce ita sam ba ta amfani da Facebook.

A cewar ta, duk shafin da aka gani da sunan ta a Facebook, to na bogi ne.

Haka kuma ta ja hankalin abokan hulɗar ta da su kula da waɗanda za su tura wa kuɗi a duk lokacin da su ke da buƙatar kasuwanci da ita.Aisha Tsamiya na yin bayani a cikin bidiyon da ta tura a yau

A saƙon bidiyon da ta fitar na tsawon minti biyu, Tsamiya ta ƙara da cewa, ”Haƙiƙanin gaskiya ni ban taɓa buɗe ‘account’ da suna na a Facebook ba, duk ‘account’ da kuma ‘pages’ da su ke a Facebook duk na ƙarya ne, ban san shi ba kuma ba ni da alaƙa da shi.”

Ta ce, ”Kwana biyu akwai abubuwan  da su ke faruwa idan na yi ‘posting’ ɗin kayayyakin da na ke sayarwa a Instagram, mutane da su ke amfani da suna na a shafin Facebook su kan yi ‘screenshot’ su ɗora kuma mutane su kan tura masu kuɗi, don haka duk wanda ya san zai sayi kaya na, ya saya ta Facebook to kar ya ɗauka cewa a guri na ya saya, ba ni da alaƙa da wannan. Don haka jama’a don Allah a kiyaye. Ni ba na Facebook, ba ni kuma da wata alaƙa da duk wani ‘page’ da ke Facebook.”

Kazalika ta ƙara da cewa, ”’Account number’ da su ka tura wa mutane GT Bank ne wanda ni kuma ‘account’ ɗin da ake tura mani kuɗi na bizines ɗi na na ‘Zenith Bank’ ne.

”In dai ba Instagram ɗin mu mutum ya bi na ‘Aisha Beauty Palace’ ba, ko kuma ‘WhatsApp number’ da na ke sawa a duk lokacin da na yi ‘posting’, don haka bayan nan babu wani. Kar wani ya tura kuɗin sa ya zo ya na gaya min cewa ‘na sai kaya ta Facebook na tura miki kuɗi an damfare ni ko an cuce ni.’ Idan ka tura ba ni ka tura wa ba. A kiyaye.”

Labarai Makamanta