Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara a kan Tsaro, Babagana Manguno ya baiyana sunayen ƙungiyoyin da su ke ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Da ya ke jawabi a yayin buɗe taron horo karo na 14 ga gamaiyar ƙungiyoyin malamai, masu wa’azi da limamai na ƙasashen Afirka da ke kan Sahara a Abuja, Manguno ya lissafo ƙungiyoyin da Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin, Ƙungiyar Tallafawa Addinin Musulunci, JNIM da kuma Ƙungiyar Musulmi ta Ƙasashen Sahara, ISGS.
Ya ce duk aiyukan ƴan ta’addan da ke addabar Afirka tun shekarar 2016, ya na samun tallafi ne daga Ƙungiyar Musulmi ta Ƙasashen Sahara, ISGS, wacce ta ke aiyukan ta a Mali, da kuma ƙasashe irin su Nijer da kuma Burkina Faso.
“Sannan sai kuma su Nasr al-Islam Wal Muslimin, Ƙungiyar Tallafawa Addinin Musulunci su ke ƙara ƙarfafa aiyukan su, inda hakan ke ci gaba da haifar da razani na zaman lafiyar yankunan.
“A Nijeriya kuma, Boko Haram da ISWAP ne su ka mamaye aiyukan ƴan ta’adda a Arewa-maso-Gabas na kasar nan,”
Manguno ya ƙara da cewa dole ne a hada kai a yaƙi aiyukan ƴan ta’adda, inda ya ce babu wata bindiga da ta fi wayar da kai da bada ilimi tun daga tushe karfi.
You must log in to post a comment.