An Zargi Hadiza Da Laifin Rashin Kunya Ga Manya

Rikicin cikin gidan da ake yi tsakanin shugabar NPA, Hadiza Bala Usman da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya na neman ya dauki wani irin yanayi. Inda Ministan ya yi ƙari akan zargin da yake yi wa tsohuwar shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa NPA na kin dawo da Naira biliyan 165 a asusun gwamnati na CFR.

Wani cikin ‘yan kwamitin da aka kafa ya shaida wa manema labarai cewa yanzu za su maida hankali ne a kan zargin Hadiza Bala Usman da laifin rashin kunya, da tsiwa ga manya.

“Muna kallon abubuwa biyu, na farko shugabar ta kasance ta na magana da shugaban kasa kai-tsaye, ta na watsi da ofishin mai girma Minista.” Inji Majiyar.

“Wannan babban rashin kunya ne da saba tsarin dokar aiki. Wannan ya isa ya sa a tsige ta.” “Na biyu, Minista ya ba ta umarni ta dawo da kwangilolin Intel da aka dakatar ko aka kashe. Abin da ba ta sani ba shi ne, har shugaban kasa ya san da maganar.”

“Ba ta yi abin da aka umarce ta ba. Wannan saba wa maganar manya ne, ba ta fi karfin a horas da ita ba.”

Labarai Makamanta