An Yi Nasarar Damke Shugaban EFCC Na Bogi

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wani mutum ya shiga hannun hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya bisa laifin sajewa da yin ikrarin shine shugaban hukumar.

Wannan batu dai na fitowa ne daga cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar a shafinta na Facebook, inda ta bayyana yadda ta yi caraf ta kama mutumin. A cewar EFCC, ta kama Salman Umar Hudu a ranar Talata 14 ga watan Faburairu, 2023 a wani otal na Abuja, bayan samun bayanan abin da yake aikatawa.

Ta bayyana cewa, Salman na gabatar da kansa a matsayin shugaban hukumar ta EFCC Abdulrasheed Bawa da dama dai gabatar da kansa a matsayin sauran jami’ai na hukumar na daban.

Da aka bincika, an gano Salman ya damfari wani mutum sama da N100,000 ta hanyar nuna masa zai warware masa wata matsala mai alaka da EFCC. An ce an samu cikakkun bayanai da za su taimaka wajen gurfanar da Salman, kuma za a kai shi gaban shari’a bayan kammala cikakken bincike.

Labarai Makamanta

Leave a Reply