An Yi Nasarar Dakushe Karfin ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Katsina

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnatin jihar a ranar Alhamis tace yan bindiga sun kashe mutum 213, sun sace 676 a faɗin kananan hukumomin da matsalar tsaro ta shafa, jihar a faɗin Jihar.

Gwamnatin jihar na cewa yan bindigan sun aikata wannan ta’adi ne tsakanin watan Yuli zuwa Octoba, 2021. Gwamnatin ta kara da cewa a wannan tsawon lokacin jami’an tsaro sun samu nasarar damke mutum 724 da ake zargi da aikata ta’addanci kan mutane a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, shine ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai game da cigaban da aka samu a dokar tsaro da gwamna ya sanya wa hannu.

Sakataren yace mutum 296 daga cikin waɗan da ake zargi suna gaban alkali, yayin da jami’an tsaro ke cigaba da binciken wasu 75. Inuwa yace: “A baki ɗaya alkaluman ayyukan yan bindiga, garkuwa da mutane da satar dabbobi daga farkon wannan doka zuwa yau, an samu raguwan kai hare-hare.”

“Alal misali, a tsawon lokacin daga watan Yuli zuwa Agusta, mun samu rahoton sace mutane 173, wanda ya rutsa da mutum 475. Daga Satumba zuwa Oktoba an samu 61, ya rutsa da mutum 201.”

“Yan bindiga sun kai hari sau 97 a watan Yuli zuwa Agusta, mutum 130 suka mutu wasu 56 suka jikkata, Haka kuma sun kai hari 56 daga Satumba zuwa Oktoba, 83 sun mutu wasu 58 sun jikkata.”

Sakataren ya cigaba da cewa: “An cafke mutum 480 da ake zargi tsakanin watan Maris zuwa Satumba, 42 na karkashin bincike yayin da aka gurfanar da 216.” “Daga watan Satumba zuwa yanzun, jami’ai sun damke waɗan da ake zargi 244, 33 na karkashin bincike yayin da 80 ke gaban kotu.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply