An Yi Nasarar Ceto Dukkanin Ɗaliban Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Ƙanƙara – Masari

Rahotannin dake shigowa daga jihar Katsina na bayyana cewar an sako daliban makanratar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 340 cikin daren jiya.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai a birnin Katsina.

“Kawo yanzu, an bamu dalibai 340, daga baya an kara da 4, yanzu akwai dalibai 344 dake hanyarsu ta zuwa Katsina yanzu,” Masari ya bayyana.

Yayinda da aka tambayeshi shin su kenan ko akwai saura, Masari ya ce gaskiya sai sun dawo, amma ‘yan bindigan sun ce sun saki dukkan yaran dake hannunsu.

“Sai sun dawo, sun ce mana sun saki dukkan yaran da ke hannunsu. Sai mun ji daga wajen iyaye ko akwai wanda bai ga dansa ba.”

“Ba mu kashe ko Naira ba, wajen kubutar da Daliban da aka sace a Kankara”.

Gwamnan ya ce Miyetti Allah da kungiyar MACBAN ne suka shiga gaba-gaba wajen tattaunawa don ganin an sako daliban kuma ba a biya ko sisi ba.

Gwamnan ya ce akwai Likitocin da aka ajiye domin kula da daliban don a tabbatar da lafiyar su kafin daga baya a mika su ga iyayensu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply