An Yi Kunnen Doki Tsakanin Real Madrid Da Chelsea A Gasar Nahiyar Turai

An Yi Kunnen Doki (1-1) Tsakanin Real Madrid Da Chelsea A Wasan Kusa Da Na Karshe Na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

Real ta kara da Chelsea karo uku ba ta taba samun nasara a kan kungiyar Stamford Bridge ba, ita ce wadda Real ta kasa ci a gasar zakarun Turai.

Sun fafata a 1971 a Cup Winners Cup inda suka tashi 1-1 a wasan farko a na biyu kuwa Chelsea ta yi nasara da ci 2-1.

Wannan shi ne wasa na 163 a Uefa Champions League tsakanin kungiyar Ingila da ta Spaniya, inda a wasa bakwai baya kungiyoyin Ingila sun yi nasara a hudu da canjaras biyu da rashin nasara daya.

Wannan shi ne karo na takwas da Chelsea za ta buga karawar daf da karshe a Champions League, ita kuwa Real Madrid za ta fafata ne karo na 14.

Wasa daya Chelsea ta yi rashin nasara a fafatawa bakwai a wasan farko na daf da karshe a Champions League, inda ta ci biyu da canjaras hudu, sai Monaco da ta doke ta 3-1 a 2003/04.

Real Madrid ta ci wasan zagayen farko tara daga 10 a Champions League karawar zagaye na biyu da rashin nasara a wasa daya.

Wannan shi ne wasan farko da Real za ta yi na daf da karshe tun 2017/18, inda ta yi nasara a wasan farko da ci 2-1 a gidan Bayern Munich.

Zinedine Zidane da kuma Thomas Tuchel suna daga cikin koci 24 da suka ja ragamar wasa sama da 15 tun daga zagaye na biyu a Champions League.

Kocin Chelsea, Thomas Tuchel ya fusaknci Real Madrid ba tare da rashin nasara ba a Champions League sau hudu, inda ya ci daya da canjaras uku.

A tarihin gasar Champions League wani kocin da ya fuskanci Real sau hudu ba tare da ta yi nasara a kansa ba shi ne Gerard Houllier da ya yi nasara a biyu da canjaras biyu.

Labarai Makamanta