An Yi Kunnen Doki A Wasan Kano Pillars Da Warri

Warri Wolves da Kano Pillars sun tashi 1-1 a wasan mako na 20 a gasar Firimiyar Najeriya da suka fafata ranar Lahadi.

Kungiyoyin sun kammala minti 45 ba tare da kwall ya shiga raga ba a wasan da Warri ta karbi bakunci.

Bayan da suka yi hutu ne suka koma zagaye na biyu, Pillars ta ci kwallo ta hannun Auwalu Malam Ali.

Saura minti hudu a tashi daga fafatawar Warri ta farke ta hannun Mark Daniel a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Da wannan sakamakon Pillrs tana mataki na biyu da maki 37, iri daya da na Akwa United wadda take ta daya a kan teburin bana, bayan buga wasanni 20 kowacce.

Kada ce ta uku a kan teburin Firimiyar Najeriya mai maki 36, sai Rivers United mai maki 35 a mataki na hudu.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga:

  • Rangers 2-0 Enyimba
  • Akwa Utd 2-1 Sunshine Stars
  • Rivers Utd 2-0 Dakkada
  • Nasarawa Utd 2-1 Kwara Utd
  • Katsina Utd 5-1 Wikki
  • Plateau Utd 2-1 Abia Warriors
  • Adamawa Utd 0-1 Heartland

Labarai Makamanta