An Tura ‘Yan Sandan Kwantar Tarzoma Jihar Oyo

Shugaban ‘yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya ba da umarnin tura rundunoni hudu na ‘yan sandan kwantar da tarzoma don magance rikice-rikicen da ke faruwa a wasu sassan jihar Oyo domin shawo kan Matsalar.

Rundunonin ‘yan Sandan masu shiga tsakanin sun haɗa da rundunar kwantar da tarzomar ƙarƙashin Ofishin Jami’an leken Asirin na kasa da kuma sashin jirage masu saukar ungulu dake kula da sa-ido daga sashen jigilar ‘yan sanda.

Jihar ta Oyo ta kasance cikin rikici a kwanan nan, ciki har da kashe-kashen da ake zargin makiyaya da yi wa manoma, sace mutane da rikici tsakanin wasu ‘yan kasuwar Hausawa da Yarbawa a kasuwar Shasha.

Amma mai magana da yawun rundunar, CP Frank Mba, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai taken, “Oyo crisis: IGP deploys intervention and stabilization forces” ya ce jami’an za su karfafa tsaro da kuma karfafa gwiwar jama’a kan yankunan da rikicin ya shafa.

Sanarwar ta ce, Rundunonin wadanda suka kunshi yawancin bayanan leken asiri da kayan aiki na rundunar, sun hada da rundunoni hudu na ‘yan sanda masu motsi, da kwararrun jami’ai daga Ofishin Leken Asirin na ‘yan sanda.

Hakazalika sanarwar ta kare da cewa, an tura “helikoptar ‘yan sanda na aiki/sa ido daga sashen ‘yan sanda na Sashin Sama.”

“Mataimakin Shugaban rundunar Sufeto Janar na ‘yan sanda, David Folawiyo ne ya ke jagorantar rundunar da za ta shiga tsakani, wanda ake sa ran zai tattara duk masu ruwa da tsaki don cimma nasarar rundunar.”

Sanarwar ta ce Shugaban ‘yan Sandan ya bayar da tabbacin cewa rundunar ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa a jihar.

Labarai Makamanta