Rahotannin dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta girke ƙarin jami’an tsaro domin tabbatar da komai ya tafi daidai gabanin ziyarar shugaba Buhari a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, shi ya tabbatar wa manema labarai hakan a Yola ranar Asabar.
Ya ce sun bukaci jami’an da su nuna ƙwarewa da kuma mutunta ‘yancin dan adam yayin gudanar da aiki.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa Buhari zai ziyarci jihar ne a ranar Litinin domin kaddamar da ƴakin neman zaɓen ‘yar takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC Sanata Aishatu Binani.
Kakakin ‘yan sandan ya ce ƙarin jami’ai da girke sun haɗar da rundunonin jami’an tsaro da jami’an sashin ƴaki da ta’addanci da kuma motocin samame.
You must log in to post a comment.