An Shiga Yaƙin Cacar Baki Tsakanin Gwamnan Bauchi Dana Binuwai

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya bayyana bacin ransa kan takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda ya fito fili ya goyi bayan Fulani Makiyaya su rinƙa yawo da Bindigogi da sunan kare kai, inda ya daura masa laifin halin da Fulani makiyaya ke ciki na ta’addanci a Najeriya musamman yankin Arewa.

Anashi ɓangaren Yayin magana da yayi da manema labarai ranar Alhamis, gwamna Bala ya tuhumi Ortom da tsananta rikicin manoma da Makiyaya ta irin maganganun da yake yi.

Amma mai magana da yawun Ortom, Terver Akase, a martaninsa, ya ce gwamna Ortom ya yi mamakin kalaman gwamna Bala saboda yana kira ga sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya da ya rantse zai kare.

Ya ce yawancin kalaman da Bala Mohammed yayi kawai yana kokarin kare Fulani Makiyaya ne. Yace: “Gwamna Ortom ya na mamakin shin wani sashen dokokin kasa gwamnan Bauchi ya dogara da shi na goyon bayan Makiyaya masu yawo da manyan makamai.”

“Abin takaicin da ke damun gwamna (Ortom) shine wai ya za’ayi mutumin da aka ba hakkin kare jama’a ya rika kalaman batar da mutane.” “Ya jaddada cewa akwai bukatan shugabanni su yi hattara wajen yin abubuwan da ka iya kai kasar nan ga halaka.”

A wani labarin na daban Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai tsinanawa yan Nijeriya wani abin azo a gani ba a bangaren tsaro.

Ya yi kira ga shugaban kasar ya sake bitar dokokin ECOWAS na zirga-zirgan mutane, hada-hadar kayayyaki da ayyuka a yankin Afirka ta Yamma.

Gwamnan ya ce makiyaya daga kasashen ketare suna amfani da damar da dokar ECOWAS din ta basu don shigowa Nijeriya su janyo rikici.

Labarai Makamanta