An Shiga Wahalar Ƙarancin Nama Da Kayan Miya A Kudancin Najeriya

Kudancin Najeriya na fuskantar matsanancin karancin Nama, Albasa, Tumatur da saran kayan Gwari.

Hakan na zuwane bayan da kungiyar dake kai irin wadannan kayan kudu, AUFCDN ta yi barazanar daina kaisu daga nan zuwa Ranar Laraba.

Shugaban Kungiyar, Muhammad Tahir ne ya bayyana haka inda yace sun tafka gagarumar Asara saboda rikice-rikice a yankin, yace suna neman gwamnatin tarayya ta basu diyyar Biliyan 475 idan ana so su ci gaba da aiki.

Yace sun aikewa fadar shugaban kasa takardun koke sau da dama amma ba’a kulasu ba, yace dan haka gargadi na karshe da zasu bayar shine daga nan zuwa 24 ga watan Fabrairu, Ranar Laraba me zuwa idan ba’a biya musu bukatarsu na zasu daina kai kaya kudu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply