An Shiga Tone-Tone Tsakanin Hadiza Bala Da Sanata Binta Garba

Dakatacciyar shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa NPA, Hadiza Bala Usman ta yi martani ga tsohuwar mamba a hukumar, Sanata Binta Garba wacce ta zargeta da wadaka da kudaden hukumar jim kaɗan bayan dakatar da ita da aka yi.

Sanata Binta Garba ta zargi Hadiza Bala Usman da assasa korarta daga hukumar tashoshin jiragen ruwa NPA a kan yadda ta nuna rashin amincewarta da rahotannin shige da ficen kudade.

A yayin martani, dakatacciyar shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwan NPA Hadiza Bala a wata takarda da ta sa hannu a ranar Litinin, ta musanta zargin da Binta Garba ke yi mata inda tace Sanatan ta je hukumar ne domin ɗaiɗaita ta ba wai kawo cigaba ba.

Kamar yadda wani sashi na takardar ta sanar, “Baya ga cewa Sanata Binta bata fadi wani abu mai muhimmanci ba, ta tsaya ne tana fadin zargi marasa tushe a takardar da ta fitar ta ranar Lahadi, ta bada kanta inda ta nuna cewa ta shiga hukumar tashoshin jiragen ruwa NPA ne domin kawai ɗaiɗaicewa a maimakon kawo cigaba.

“Kamar yadda nace, ta dogara ne da zargin cewa ta jajirce a kan yadda kudi ke shiga da fita a hukumar ta NPA wanda duk karya ne, cike da kwarin guiwa tun daga 2016 na sanar da cewa hukumar NPA na shirye domin karbar kowanne irin kalubale daga jama’a.”

A yayin bayani kai tsaye, Hadiza Bala Usman tace hukumar karkashin mulkinta ta dauki matakai masu yawa wurin tabbatar da cewa komai a bayyane yake a hukumar.

A don haka Hadiza Usman ta kalubanci ikirarin sanatan inda tace me yasa a lokacin bata rubuta takarda ba domin kalubalantar ta. “A don haka akwai wasu tambayoyi da ya dace sanatan ta amsa: A lokacin da masu kididdige shige da ficen kudi suka gabatarwa kwamitin kudi rahoto kuma tana mamba, me yasa bata nemi karin bayani ba?

“Idan kuma ta nema me ya faru? Da bata gamsu da tambayoyin da tayi ba me ya hana ta rubuta koke ko korafi? Me yasa sai a halin yanzu take maganar?”

Labarai Makamanta