An Shiga Takun Saƙa Tsakanin Ɗangote Da Isiyaka Rabi’u

Kamfanin BUA mallakar sanannen ɗan kasuwar nan Alhaji Abdulsamad Isiyaka Rabi’u ya mayar da martani kan ikirarin kamfanin Dangote da kamfanin Flour Mill cewa matatar sukarin BUA dake garin Fatakwal matsala ce ga kamfanonin sukari a Najeriya.

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da shugaban Flour Mill, John Coumantaros, sun aike wasika ga Ministan kasuwanci da masana’antu inda suka tuhumi matatar sukarin BUA na saɓa tsarin sukari na Najeriya (NSMP).

Tsarin NSMP wani shiri ne da aka yi a 2013 na tabbatar da cewa Najeriya ta samu isasshen sukari da zai isa al’umma.

Martani kan hakan, shugaban BUA AbdulSamad Rabiu ya ce matatar sukarinsa na bin ka’idar NEPZA da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu. Isyaka Rabiu ya ce Dangote da Coumantaros na kokarin “fito-na-fito da umurnin shugaban kasa da kuma mutuncin ma’aikatar kasuwanci da masana’antu.”

“Saboda haka muna ganin wannan fito-na-fito ne ga ikon shugaban kasa da kuma yunkurin raina hankalin Najeriya da ma’aikatunta da kuma kokarin dakile abokan takara, don su zama su kadai ke kasuwancin sukari kuma kasar ta wahala,”.

Kowa ya san cewa “a Najeriya da duniya, duk inda Dangote yake harka ko kasuwanci bai san ganin kowa a wajen kuma ya kan yi iyakan kokarinsa wajen dakile mutum” kuma “hakan yake sake yi yanzu.”

Wasikar Dangote A wasikar mai dauke da kwanan watan 8 ga Junairu 2021, Dangote da Coumantaros, sun aike wasika ga minista Niyi Adebayo, inda suka zargi matatar sukarin dake Fatakwal da cewa an ginata ne domin sabawa tsarin NSMP.

Sun bukaci Ministan ya binciki adadin danyen sukarin da BUA ke kawowa Najeriya kuma ya ci su tarar da ya kamata.

Labarai Makamanta