An Shiga Ruɗani Sakamakon Ƙarin Kuɗi Na Sirri Da Kamfanonin Lantarki Suka Yi

Jama’ar Najeriya masu amfani da wutar lantarki sun shiga cikin ruɗani biyo bayan wani ƙarin kudin wuta na bazata da kamfanonin raba wutar lantarki suka yi kashi 100 bisa 100 cikin sirri.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewar ƙarin kuɗin wutar an yi shine tun a ranar Talatar makon da ya gabata, amma al’umma basu farga da hakan ba sai a ranar Litinin ta wannan makon da muke ciki, biyo bayan wahalar da suka rinƙa fuskanta a wajen sanya katin Mita da suka saya.

Ya bayyana cewar waɗanda suka sayi katin mita na N5,000 a Talatar makon da ya gabata sun gaza sanya katin da suka saya daga Kamfanin.

Wakilimu ya bayyana mana cewar duk lokacin da aka yi kokarin loda katin sai sakon ya bayyana cewar ka sake maimaitawa, wanda hakan ke nuna cewar da akwai matsala ta network, ashe ba hakan bane dalilin ƙarin kuɗin wutar ne.

Lokacin da wakilimu ya ziyarci cibiyar raba wutar lantarki domin gabatar da korafi akai, ya tarar da sama da mutane 500 waɗanda suke kan layi domin shigar da irin korafin da ya kai.

Daga bisani wakilinmu namu ya samu nasarar gabatar da korafin nashi bayan tsawon awannin, inda aka bashi hakuri da bada tabbacin shawo kan matsalar nan bada dadewa ba.

Daga bisani katin ya shiga bayan tsawon lokaci, sai dai abin mamaki maimakon samun unit 200 sai ya samu 100.8, dalilin da yasa ya sake komawa Ofishin kamfanin bayan tsawon lokaci ya samu ganawa da wani jami’in Kamfanin, inda ya tabbatar mishi da cewar ƙarin kuɗin wutar da aka yi mishi ya karu da kashi 100.

“Tun asali wannan shine dalilin da ya sa ka kasa sanya katin da ka sanya saboda karin da aka yi da kuma wasu sauye sauye da aka samu sakamakon karin”.

Wasu daga cikin jama’ar da aka zanta dasu sun bayyana fuskantar irin wannan matsalar sakamakon ƙarin kuɗin bazata da kamfanonin suka yi.

“Kafin wannan lokaci ya kasance ina sayen unit 100 akan N2,500, amma abin mamaki shine a yanzu an bani 51.2 ne, abin damuwar ma shine bari na cikin duhu da aka yi na rashin sanin gaskiyar lamari har sai da na ziyarci kamfanin.

“Ƙarin abin haushi tun a ranar Larabar makon jiya nake kiransu ina korafi, amma maimakon su gaya mini gaskiya sai suka cigaba da yaudara ta da cewar in binciki batirin mita ta, da sauran karairayi”

“Hakan ya sanya nayi ta zirga-zirga zuwa kamfanin kafin daga bisani nake samun bayanin dukkanin wannan matsala da nake ciki ta biyo bayan ƙarin kuɗin wutar da aka yi ne na bazata cikin sirri, inji ɗaya daga mutanen.

Dukkanin ƙoƙarin da akayi na ganin mai magana da yawun kamfanin abin ya ci tura, sakamakon kin ɗaukar kiran wayar da aka yi mishi da kuma ƙin amsa sakon kar ta kwana da aka aike mishi dashi.

Labarai Makamanta