An Shiga Makoki Sakamakon Yawaitar Kashe-Kashe A Kudancin Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewar duba ga hauhawan matsalar rashin tsaro a jihar kungiyar shugabannin kirista a kudancin Kaduna sun kafa wani kwamitin mutum hudu don taron addu’a na wannan shekarar.

Tsawon shekaru biyu kenan ba a gudanar da taron addu’an ba wanda aka saba yi duk shekara saboda annobar korona, da sauran kalubale na rashin tsaro.

Da yake rantsar da kwamitin a ranar Laraba a garin Kafanchan, jim kadan bayan taron mika masa shugabanci, shugaban kungiyar, Dr. Emmanuel Kure, ya bukaci mambobin kwamitin da su jajirce wajen ganin an cimma nasara a taron.

Ya bayyana taron addu’an a matsayin mai muhimmanci, cewa za a yi addu’o’i domin dawo da yancin yankin da jiha dama kasa baki daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply