An Shiga Binciken Gaskiyar Zargin Ko Malami Na Sarrafa EFCC

Hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa taannati ta ce tana gudanar da bincike kan zargin cewa ministan shariar ƙasar, Abubakar Malami ne yake sarrafa hukumar, sai abin da ya ce ta ke yi.

Binciken EFCC ya shafi wani sautin da ake yadawa ne ta intanet wanda a ciki ake zargin cewa Malami ne yake juya hukumar a binciken da ta ke gudanarwa da ya shafi cin hanci da rashawa.

Hukumar EFCC ta ambato wani jami`inta mai suna Mohammed Idris, wanda ɗan sanda ne kuma ƙwararren lauya cewa shi ne yake tattaunawa da wani da ake zargin cewa mai laifi ne ta waya.

Hukumar ta ce ta saurari sautin da ake magana wanda jaridar Daily Nigeria ta bankaɗo, kuma ta fahimci cewa jaminta ne yake magana da wani abokin cin mushe ko cuwa-cuwarsa, wanda a ciki yake cewa minstan sharaa Abubakar Malami shi ke da wuka da nama a EFCC, kuma komi girman rikici zai kashe maganar idan aka kama kafarsa.

Labarai Makamanta