An Samar Da Kwararan Matakai Wajen Magance Matsalar Lantarki – Minista

Gwamnatin Nijeriya ta ce an samu nasarar maido da wutar lantarki bayan katsewarta a farkon makon nan, lamarin da ya jefa kasar cikin duhu, sakamamon karancin gas da kuma ayyukan masu fasa bututun dake samar da gas ga manyan tashoshin samar da wutar lantarki.

Sanarwa dake dauke da sa hannun Ministan Lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu da aka fitar yau Asabar ta kara da cewa, an samu nasarar gyara bututan gas da aka lalata a babbar tashar lantarki ta Okpai, wanda hakan ya samar karin wutar lantarki da ake samu.

Ministan ya kuma kara da cewa, ana daf da kammala gyaran dukkan rashohin wutar lantarki da suka dakatar da aiki sakamakon gyara su da aka saba yi daga lokaci zuwa lokaci.

Sanarwar ta kara da cewa, an amince akan sabon tsari da farashin gas da za a rika baiwa kamfanoni da suke da tashoshin samar da wutar lantarki, ta yadda zasu ci gaba da aiki ba tare da bata lokaci ba.

Injiniya Abubakar Aliyu yace, gwamnati ta shi tsaye wajen ganin an magance dukkan matsalolin da suke kawo koma baya ga harkar wutar lantarki da suka hada da; karancin gas, fasa bututan gas da kuma gyara wasu tashohin lantarki.

Cikin sanarwar ministan ya bayyana cewa tun daga ranar 14 ga wannan watan masu ruwa da tsaki suke ci gaba da aiki tukuru domin ganin cewa irin wannan matsala bata sake faruwa ba.

Ministan ya kuma ce ana aiwatar da sabbin matakan da aka amince da su domin hana sake aukuwar wannan matsala, yana mai tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa, kokarin inganta samar da wutar lantarki da gwamnati take yi zai ci gaba.

Labarai Makamanta