An Sake Bankado Zunubban Abba Kyari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta bankaÉ—o wasu kadarori 14 mallakar tsohon shugaban rundunar tattara bayanan sirri ta hukumar ‘yan sandan kasar DCP Abba Kyari.

An ruwaito cewa kadarorin sun hadar da manyan kantunan sayayya, da gidaje, da filin wasan polo, da filaye tare kuma da gonaki.

An zargi Kyari da kin bayyana kadarorin nasa dake wurare daban-daban a birnin Tarayya, Abuja da birnin Maiduguri na jihar Borno.

An kuma gano sama da naira miliyan 207 da euro 17,598 a asusun ajiyarsa na bankunan GTB, da UBA, da kuma bankin Sterling.

Haka kuma gwamnatin tarayya ta shigar da wasu tuhume-tuhume daban guda 24 a kan Sunday Ubua, tsohon mataimakin Abba Kyarin, wanda shi ma tuni aka dakatar da shi.

Labarai Makamanta