An Rantsar Da Samia Hassan Shugabar Tanzaniya


An rantsar da Samia Suluhu Hassan a matsayin mace ta farko Shugaabar Ƙasar Tanzania biyo bayan mutuwar John Magufuli ranar Laraba.

Alƙalin Alƙalai Ibrahim Juma ne ya rantsar da ita a Fadar Gwamnati da ke babban birnin ƙasar Dar es Salaam.

Ita ce shugabar Tanzania ta shida bayan ta shafe shekara fiye da biyar a matsayin mataimakiyar Magufuli, wanda ya rasu sakamakon ciwon zuciya.

Kundin tsarin mulkin Tanzania ya tanadi cewa mai shekara 61 ɗin za ta ƙarasa wa’adi na biyu na shekara biyar da suka fara.

Ita ce shugabar ƙasa mace tilo a Nahiyar Afirka da ke kan mulki yanzu haka.

Labarai Makamanta