An Naɗa Ngozi Iweala Shugabar Hukumar Cinikayya Ta Duniya

An nada Mrs Ngozi Okonjo Iweala a matsayin shugaba Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO).

Sanarwar nadin Okonjo-Iweala ya fito ne daga bakin hukumar da ke Geneva a ranar Litinin 15 ga watan Fabrairu.

Okonjo Iweala ce mace ta farko kuma bakar fata da ta fara shugabancin hukumar. Wa’adinta zai fara ne daga ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2021.

Wakilai daga kasashe 164 da ke kungiyar ne suka jefa kuri’a kafin nadin na Okonjo-Iweala kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar.

An nada Okonjo-Iweala ne bayan sabon shugaban kasar Amurka Joe Biden ya goyi bayan nadinta wadda tsohon shugaba Donald Trump ya dakile.

Labarai Makamanta