An Naɗa Lalong Sarkin Yaƙin Zaɓen Tinubu

Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya sanarwa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa a ranar Alhamis an tabbatarwa gwamnan Filato Simon Lalong mukamin Darektan Kamfen din Tinubu Da Kashim Shettima.

” Ba a nada ni shugaban kamfen din Tinuba ba wai don ni kirista ne ba, an nada ni saboda cancanta ta da kuma dacewa da na yi in jagoranci wannan tafiya.

” Da farko dai ni ne shugaban gwamnonin Arewa, sannan kuma ni mutum ne mai kishin jam’iyyar APC wanda babu na biyun sa, saboda haka na cancanta kuma ba zan ba ku kun ya ba.

Jam’iyyar APC ta ce ta nada Lalong darekta Janar din Kamfen din Tinubu ne saboda cancantar sa da kuma kishin jam’iyya da yake da ita, Sannan kuma shi mutum ne dake cika aiki.

Nan da watanni biyu masu zuwa za a fantasma Kamfen a fadin kasar nan. Jam’iyyat APC ta gamu da mummunar adawa daga wasu faga cikin jigajigan ta saboda Muslim-Muslim ticket da take yi, wato dan takarar shugaba kasa Musulmi, mataimaki musulmi.

Labarai Makamanta