An Kuma: Gini Ya Sake Ruftawa Da Mutane A Legas

Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewa wani gini da ake cikin aikin gina shi ya kife a Magbon, yankin Badagry, jihar Legas ranar Laraba, inda ake tsammanin mutum hudu sun mutu nan take.

Hakanan kuma an zaro wasu mutum biyar ɗauke da raunuka kala daban-daban, yayin da jami’ai ke cigaba da aikin ceto sauran dake kasan baraguzan ginin.

Wannan na zuwa ne bayan dogon gini mai hawa 21 ya kife a jihar a farkon wannan watan, inda mutane da dama suka hallaka ciki har da mamallakin ginin.

Daraktan hukumar kashe gobara (Kwana-kwana) ta jihar Legas, Margret Adeseye, ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Ta bayyana cewa tuni jami’an kwana-kwana da masu aikin ceto na ofishin Badagry, suka dira wurin jim kaɗan bayan samun rahoton lamarin. Daraktan tace:

“Mun samu rahoton rushewar wani gini a Badagry, jahar Legas. Tuni jami’an kwana-kwana suka ceto mutum 5, yayin da ake cigaba da aikin ceto sauran waɗan da ginin ya rufta wa.” “Mafi yawan mutanen da lamarin ya shafa masu aikin gini ne a wurin, kuma an zaro su da rauni daban-daban amma suna cikin hayyacinsu, an garzaya da su asibiti.”

“A halin yanzun an ciro wasu mutum hudu ko motsi basu yi, kuma zuwa yanzun jami’an yan sanda da yan kwana-kwana na cigaba da aiki a wurin.”

Labarai Makamanta