An Koreni Daga Aiki Bisa Zargin Na Gana Da Atiku A Dubai – Onnoghen

Tsohon alkalin alkalai, Mai shari’a Walter Onnoghen, ya bayyana dalilin da yasa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sallameshi daga aiki.

Onnoghen, wanda aka zarga da kin bayyana kadarorinsa tare da mallakar asusun banki a ketare, an sallameshi daga aiki ana sauran makwanni kadan kafin zaben shugaban kasa a 2019.

An ruwaito cewa, daga bisani kotu ta musamman ta CCT ta yanke masa hukuncin haramta rike ofishin gwamnati na tsawon shekaru 10.

Sallamar Onnoghen ta janyo maganganu daban-daban inda wasu jama’a ke kallon hakan da siyasa zalla.

Amma kuma, a yayin kaddamar da wani littafi a Abuja a ranar Juma’a, Onnoghen yace ba a taba fuskantarsa da wani zargi ba kafin a dakatar da shi.

Yace bayan rade-radin cewa ya samu ganawa da Atiku a Dubai, shugaban kasa Buhari bai bashi damar kare kansa ba. “An yi ta rade-radin cewa na gana da Atiku a Dubai.

Amma a yanzu da nake magana, ban taba haduwa ni da Atiku ba a rayuwata. Kamar hakan bai isa ba, an zargeni da sakin manyan ‘yan ta’adda.

Labarai Makamanta