An Kashe Malamai 10 Da Garkuwa Da 50 A Kaduna – Kungiyar Malamai

Kungiyar malaman sakandare a Najeriya reshen Jihar Kaduna ta ce ‘yan bindiga sun kashe mambobinta malaman makaranta 10 sannan sun yi garkuwa da wasu malamai 50 a fadin kananan hukumomin jihar 23 daga watan Janairu zuwa yanzu.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnan jihar Nasiru El-Rufai da yayi amfani da ikon da yake da shi domin ceto malaman da kuma sauran wadanda ‘yan bindiga ke ci gaba da tsare wa.

Shugaban kungiyar na JIhar Kaduna, Ishaya Dauda ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labara da yayi a Kaduna, cikin abubuwan da kungiyar ta yi domin zagoyowar ranar malamai ta duniya da aka yi a ranar Laraba.

Shugaban ya ce malaman sakandare 10 ne suka rasa rayukansu a hannun ‘yan bindigar, kana sama da 50 kuma na hannun ‘yan bindigar kuma har yanzu ba a sako ko da daya daga cikinsu ba.

Labarai Makamanta