An Kara Wa’adin Shugabancin Babban Sifeton ‘Yan Sanda

Ministan harkokin ‘yan sanda Mohammed Maigari Dingyadi, ya ce babban sifeton ‘yan sandan ƙasar Usman Baba Alkali, ba zai yi ritaya a lokacin tsakiyar zaɓukan ƙasar da ke tafe, kamar yadda ake tsammani.

Ministan na wannan maganar ne yayin da yake amsa tambayar manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar jim ƙadan bayan kammala taron majalisar zartawar ƙasar.

Dingyadi – wanda ya ce tuni babban sifeton ‘yan sandan ya karɓi takardar tsawaita aikinsa – ya ƙara da cewa sabuwar dokar aikin ‘yan sanda ta 2020 ta sauya tsarin ritayar sifeton ‘yan sandan.

Wasu kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa babban sifeton zai cika shekara 60 ranar 1 ga watan Maris mai zuwa kwanaki kwana huɗu bayan zaɓen shugaban ƙasar.

To sai dai yayin da yake amsa tambayar ‘yan jarida kan ko akwai yiyuwar babban sifeton ‘yan sandan zai yi ritaya a lokacin, sai ministan ya ce ”ban san inda kuka samo waɗannan bayanai ba”

”To amma bari na faɗa muku dokar aikin ‘yan sanda ta 2020 ta nuna cewa nan gaba babban sifeton ‘yan sanda zai ƙara shekara huɗu a kan muƙaminsa, kuma tuni shugaban ƙasa ya ba shi takardar tsawaita wa’adinsa, dan haka batun saukar Sifeton ‘yan sanda a lokacin tsakiyar zaɓukan ƙasa bai taso ba”, in ji ministan

Labarai Makamanta