An Kara Wa’adin Hada Layukan Waya Da Katin Dan Kasa

Labarin dake shigo mana yanzu daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta sake tsawaita wa’adin da ta diba na hada layukan wayoyi da lambar katin dan kasa zuwa ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa.

Wannan ne karo na bakwai da gwamnati ta dage lokacin datse layukan da ba a hada da lambar katin dan kasa ba, wanda ta ce hakan zai dakile hauhawar rashin tsaro a kasar nan.

Mai girma ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta kara lokaci kan wa’adin da ta diba na toshe layikan da ba a hada da lambar katin dan kasa ba.

“Ana kira ga ‘yan kasa da mazauna kasar nan da su tabbatar da sun hada kafin nan da karshen shekarar nan,” a cikin wata takarda da mai magana da yawun hukumar sadarwa ta kasa Ikechukwu Adinde da mai magana da yawun NIMC, Kayode Adegoke suka sa hannu.

Takardar ta ce wannan hukuncin karin wa’adin lokacin ya biyo bayan rokon da masu aiki da layukan wayoyi da kuma sauran masu ruwa da tsaki suka dinga yi ne, sun bukaci a kara wa’adin ne saboda a tabbatar da cewa an bi umarnin gwamnti domin gujewa toshe layukan.

“Kara wa’adin zai samar da damar yi wa ‘yan Najeriya da ke kauyuka rijista, kasashen waje, makarantu, asibitoci, wuraren bauta, bakin haure da sauransu wadanda a farko duk basu yi ba.”

Labarai Makamanta