An Kalubalanci Buhari Ya Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta’addanci

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Majalisar Jihohin Arewa ta Ansar-ud-Deen Society of Nigeria, ta bukaci Gwamnatin Buhari da ta tona asirin masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci da ‘yan ta’adda a Najeriya.

Sakataren kungiyar, Alhaji Isiaq Sanni ne ya yi wannan kiran a Kaduna lokacin da kungiyar da al’ummar Yarbawa suka karrama shugabansu marigayi Alhaji Liadi Adeyinka Olapade.

Da yake jawabi a wajen taron addu’o’in Fidau na kwana 8 da aka shirya domin karrama marigayi Alhaji Olapade, Sakataren kungiyar Ansar-ud-Deen ya ce marigayin ya rayu, ya yi aiki kuma ya mutu a kan fafutukar ganin an samu hadin kai da tabbatar da Najeriya ta hanyar bunkasa ilimin ‘yan kasa.

“Alhaji Liadi Olapade ya kasance mai taimakon jama’a, kadan daga abubuwan da muka gani sun nuna cewa ana kaunarsa sosai. Ya yi matukar kyautatawa al’ummar Ansar-ud-Deen da kuma bil’adama baki daya. “Saboda kishinsa na addini da ilimin ‘yan kasa, wanda yake cewa ita ce hanya mafi dacewa ta yaki da rashin tsaro, ya amince da nadi kuma ya wakilci Majalisar Ansar-ud-Deen ta jihohin Arewa da kyau a hukumar gudanarwar jami’ar mu.

“Abin takaici ne cewa a yau, rashin tsaro da Olapade ya yi yaki dashi ya ci gaba da wanzuwa. Don haka muna kira ga gwamnati da ta kara himma wajen yakar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro, domin kokarin da suke yi a halin yanzu bai isa a magance kalubalen ba.

Labarai Makamanta