An Kakaba Wa Kamfanonin Jiragen Ƙetare Takunkumi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta hana kamfanonin sufurin jiragen sama na ƙasashen waje taɓa kuɗaɗensu da suka kai dala miliyan 450.

Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa hukumomin Najeriya, ƙasar da ta fi saura girman tattalin arziki a Afirka, sun dakatar da fitar da kuɗaɗen ƙasar waje don sayo kaya da kuma na masu zuba jarin da ke son kai wa ƙasashensu na asali.

Gwamnati ta ɗauki matakin ne saboda ƙarancin kuɗaɗen ƙasar waje da ƙasar ke fuskanta, musamman na dalar Amurka.

Labarai Makamanta