An Kafa Kwamitin Bincikar Zunubban Hadiza Bala Usman

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi, ya kafa kwamitin mutum 11 domin binciken badakalar Hadiza Bala Usman.

An dakatar da shugabar tashoshin jiragen ruwan ne sakamakon zarginta da ake da badakalar salwantar wasu kudade har N165 biliyan.

Shugaban ayyukan da suka shafi teku, Suleiman Auwalu ne zai jagoranci kwamitin Sakamakon zargin badakalar wasu kudade da ake yi kuma ya kai ga an dakatar da manajan daraktan hukumar kula da hanyoyin shige da fice na ruwan kasar nan (NPA) Hadiza Bala Usman.

Kwamitin mutum 11 ya samu shugabancin Suleiman Auwalu, darakta ne a bangaren da ya shafi teku, sai Gabriel Fan, mataimakin darakta a bangaren shari’a, ma’aikatar sufuri ta tarayya ce zata yi aiki a matsayin sakatariyar kwamitin.

Labarai Makamanta