An Haramta ‘Yan Kato Da Gora A Jihar Kaduna

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya, reshen jahar Kaduna ta sanar da haramta ayyukan kungiyoyin matasa ‘Yan sa kai, wadanda aka fi sani da suna ‘yan kato da gora, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya ya bayyana.

Rundunar ta sanar da haramta ayyukan kungiyoyin ne ta bakin kaakakinta, DSP Yakubu Sabo cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta.

DSP Sabo ya bayyana cewa rundunar ‘Yansanda tana gargadi kada wani ya sake bayyana kansa a matsayin dan kato da gora, balle kuma ya aikata wani aiki da sunan tsaro a gaba daya jahar Kaduna.

Kakakin ya cigaba da cewa duk wanda hukumar ‘Yansanda ta kama ya karya wannan umarni zai gamu da fushin hukuma, kuma za’a yi amfani da duk hanyoyin da doka ta tanadar don hukuntashi, ko wanene.

“Don haka rundunar Yansandan jahar Kaduna take neman hadin kai da goyon bayan jama’a ta wajen bata muhimman bayanai game da ayyukan miyagu a unguwanninsu domin rundunar ta samu daman kare su yadda ya kamata.” Inji shi.

Sai dai wasu mazauna garin Kaduna suna bayyana rashin jin dadinsu da wannan doka, inda suka nuna muhimmancin ‘Yan kato da gora sakamakon sune mafi kusa da jama’a, kuma suke kai musu dauki cikin gaggawa.

Related posts