An Haramta Sayar Da Barasa A Najeriya – NAFDAC

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC ta haramta sayar da barasa da ke ƙunshe a ƙananan leda.

Ta ce daga 2024 ba za ta sake yin rijistar barasar ta leda da ƙananan kwalabe ba.

Hakan dai ba zai rasa nasaba da kuka da iyaye ke yi cewa kayan maye na lalata rayuwar yaransu ba.

Gagarumin mataki na rage yawaitar barasa da kuma dakile shan ta a kasar da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar ta dauka ya samu jinjina daga wasu daga cikin ‘yan kasar.

A yayin da wasu ke ci gaba da yin tofin Allah-tsine da dakatar da yin rajistar barasa da ke kunshe a cikin leda da kuma ƙananan kwalabe da ke da nauyi kasa da milimita 200, darakta janar a hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye, ta ce hukumar ta haramta yin rijistar sabbin abubuwan sha na barasa da ake kullawa a cikin sacet da ƙanana kwalaben gilashi.

Labarai Makamanta