Rahoton dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar wani kwamitin wanzar da zaman lafiya ya gudanar da taro da shugabannin kafafen watsa labarai a jihar.
Kwamitin yace ya hada kan masu ruwa da tsaki a fanni watsa labaran ne, don tattaunawa tare da samar da hanyoyin da za a ci gaba da wayar da kan ‘yan siyasa ta yadda za a gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
Kwamitin inganta zaman lafiyar wanda aka kafa domin samar da zaman lafiya, kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe ya gana da kafofin watsa labarai na jihar Kano, inda aka tattauna tare da bayar da shawarwarin yadda za a tunkari babban zaben 2023.
Taron ya nemi hadin kan ‘yan jarida wajen tsaftacce kalaman da ake yi a kafafen yada labaran jihar Kano musamman a wannan lokaci da ake ci gaba da yakin neman zabe, kamar yada Ambasada Ibrahim Wayya babban jami’I a kwamitin wanzar da zaman lafiya na jihar ya shaida
Malam Abubakar Salihu wanda ya wakilci shugabannin kafafen watsa labarai na jihar Kano ya ce za su tabbatar ‘yan jarida sun bi ka’idojin aikin jarida don tabbatar da zaman lafiya lokacin zabe a jihar Kano.
Kwamitin samar da zaman lafiya a jihar ya ce nan gaba zai shirya gagarumin taro inda ake fatan dukkan ‘yan takarar gwamna da shugabannin jam’iyya za su sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin yakin neman zabe da kuma lokacin zaben 2023.
You must log in to post a comment.