An Gudanar Da Sallar Rokon Ruwa A Saudiyya

Ranar Alhamis da zawali aka gudanar da Sallar rokon ruwa a Masallatan Haramain guda biyu dake Makkah da Madina daya daga cikin Limamin Haramin Makkah Sheikh Balelah ne ya jagoranci Sallar a Makkah.

Yayin da a Haramin Madina Sheikh Qasim ya jagkranci Sallar. Anyi wannan sallar ne dai saboda yadda ruwan sama ya dauke da wuri a daminar bana da nufin Allah ya shayar da alumma ruwa.

Ba a kasar Saudiyya ne kadai ake fama da daukewar ruwan saman ba, hatta anan Najeriya an samu daukewar ruwan damina da wuri, abinda yake barazanar samun amfanin gona wadatacce a cikin shekarar badi da zamu shiga.

Labarai Makamanta