An Gudanar Da Sallar Idi Cikin Ruwan Sama A Jalingo

Sakamakon saukan ruwan Sama kamar da bakin kwarya, ya jinkirta Sallar Idi Karama a Jalingo, Fadar Jihar Taraba.

Wakilinmu Bashir Adamu ya ruwaito mana cewa duk da ruwan Saman Sallar Idin ya gudana cikin Annashawa da kwanciyar hankali.

Jihar Taraba ta bi sahun sauran Jihohin Kasannan wurin gudanar da Sallar Idi Karama, duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka wayi Gari da shi a garin Jalingo.

Karamar Hukumar Lau, na daya daga cikin Kananan Hukumomi goma sha shida a Jihar da Taraba da ke yawan fuskantar matsalolin rikice- rikicen da suka hada da na Makiyaya da Manoma da kan canza salo izuwa na Addini.

Kamar ko da yaushe dai, a wannan karon ma Sallar ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana a yankin. Inda Liman Amadu Basiru ya jagoranci Sallar Idin a Garin Kunini tare da huduba ga Al’ummah da su gujewa shiga hakkokin junan su hasali tsakanin Manoma da Makiyaya.

Da yake nashi tsokaci, Mai Martaba Sarkin Lau, Abubakar Umar Sadiq, Danburam na Uku, ya hori Al’ummah da su gujewa daukar Makamai a hannunsu, suna kashe kawunansu.

Hadi Haruna Lau, tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni ne a Jihar Taraba kuma Wazirin Lau, ya nuna alhinin rashin da sukayi a Masarautar tare da kira ga Al’ummah da su gujewa bijirewa shuwagabannin su a koda yaushe, inda ya shaida nadin Shugaban Kungiyar Izala na Kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau a matsayin Santurakin Lau da Masarautar tayi.

Daga bisani an cigaba da gudanar da shagul- gular Sallar a Masarautar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply