An Gudanar Da Jana’izar Mama Taraba A Jalingo

Gawar Tsohuwar Ministan Mata, Sanata A’isha Jummai Alhassan da akewa lakani da ‘Maman Taraba’, a Ranar Litini ya iso Birnin Jalingo, Fadar Jihar Taraba daga Kasar Kairo, inda akayi Jana’izar ta a Makabartan Musulmi na Jeka- da Fari kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Da misalin kimanin Karfe biyar da mintuna goma sha daya na Yammacin Ranar Litini, Gawar Tsohuwar Ministan, ta iso Filin sauka da tashin Jiragen Sama na Danbaba Suntai dake Birnin Jalingo tare da rakiyar Iyalai makusantan Marigayiyar, Mataimakin Gwamna, Haruna Manu, sauran Yan’uwa Makusanta, abokai da aminan arziki da yawa suka karbi Gawar Marigayiyar.

Mataimakin Gwamnan a madadin Gwamnatin Jihar yayi Mata kyayyawar shaida na gaskiya da rikon amana.

Farfesa Ango Abdullahi shine Mahaifin Yara ukun da Marigayiyar ta bari a raye, ya aiyanata a matsayin mace mai akida kuma jaruma da gurbin da ta bari zaiyi wuyar cikewa.

Sanata Ibrahim Abdul’Aziz ya yane ga Marigayiyar inda yace Allah Ya baiwa Maman Taraba baiwan kaifin basira, jajircewa akan abinda ta sanya a gaba, son Jama’a da kin rashin gaskiya.

Tsohon Magatakardan Gwamnatin jihar kaduna, Lawal Sama’ila Yakawada, Sarkin Muri, Alhaji Abbas Ndjidda Tafida da sauran Sarakunan Jihar Taraba, Dan Takarar Shugabancin Jam’iyyar APC na Kasa, Muhammad Bello Mustafa, Shugaban Jam’iyyar PDP na Taraba, Laftanar Kanar Dan-Abu Kefas Ritaya, Gadiman Muri, Tukur Abba Tukur, Tsoffin Sanatocin Jihar da sauransu na daga cikin wadanda suka nuna juyayinsu bisa rasuwar Tsohuwar Ministan.

Bashir Adamu Daga Jalingo

Labarai Makamanta