An Garƙameta A Kurkuku Sakamakon Wallafa Hotunan Tsiraici

Wata kotu a kasar Ghana ta yanke wa wata fitacciya a shafin sada zumunta Rosemond Brown hukuncin zaman kaso na wata uku, sakamakon kama ta da laifin wallafa hotonta tsirara tare da danta a gefe.

Ta fashe da kuka a lokacin da alkalin kotun da ke birnin Accara ya sanar da hukuncin da aka yanke mata.

A hoton da ta wallafa tun a watan Yuli na ranar murnar zagayowar ranar haihuwa, ta fuskanci danta mai shekara bakwai tsirara kuma ta rike hannunsa, shi kuma yana sanye da dan kamfai, sannan dogon gashinta ya rufe kirjinta.

Hoton ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, inda mutane ke ta yi mata tofin Allah tsine. Duk da cewa ta nemi afuwa, amma ‘yan sanda sun gayyace ta domin amsa tambayoyi.

Kungiyar kare hakkin yara ce ta shigar da karar tare da tabbatar da an yanke mata hukuncin da ya dace da laifinta.

A ranar Laraba ne alkalin kotun ya same ta da laifin wallafa hotunan badala da cin zarafi da take hakkin sirrin wani mutum.

An dakatar da sanar da hukuncin kotun har zuwa ranar Juma’a bayan an yi mata gwajin ciki, wanda ya nuna ba ta dauke da juna biyu. Kuma kotun ta ce an yanke mata hukuncin ne domin ya zama darasi ga masu son aikata hakan.

Tuni ma’abota shafukan sada zumunta suka fitar da maudu’in #FreeAkuapemPolootare da kiran a sake ta.

Shi ma fitaccen mawakin salon raff na Ghana Sarkodie ya ce hukuncin da aka yanke mata ya yi tsanani na raba da da mahaifi.

Labarai Makamanta