An Gano Mabuyar ‘Yan Ta’adda A Birnin Tarayya Abuja

A kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a babban birnin tarayya Abuja, jami’an sojin Najeriya sun kai samame wani yankin hakar ma’adinai da ake haka ba bisa ka’ida ba. An kai farmakin ne a yankin Tukashara Wasa, Apo a tsakiyar birnin tarayya Abuja.

Wannan batu na zuwa ne ta bakin Manjo Janar Musa Danmadami, babban daraktan yada labarai na gidan tsaro a Najeriya. Ya bayyana hakan ne a wani taron bayyana nasarorin da jami’an sojin kasar suka samu cikin makwanni biyu kamar yadda aka saba a babban birnin tarayya Abuja.

Nasarar da aka samu a samamen da aka kai A cewarsa, an kama akalla mutane 60 da ake zargin suna hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba, ya kuma bayyana cewa, jami’ai sun samu damar yin wannan gagarumin aikin ne bayan da aka samu rahotannin tsaro na sirri, kuma an kwato wata babbar mota tirela makare da haramtattun kayayyaki da aka haramta.

Hakazalika, an kwato bindigogi 5, adduna 14, guduma 4, Babura 25, mota 1 da dai sauran kayayyaki da dama na aikata laifi. Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da kasar Amurka da Burtaniya ke ci gaba da bayyana gargadi ga ‘yan Najeriya kan yiwuwar samun hare-hare da za su iya aukuwa a babban birnin tarayya Abuja.

Labarai Makamanta