An Damke Mutum 6 Kan Batan Dan Jarida A Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar yan sanda ta kasa ta ce ta kama mutum shida bayan batan dan jaridan nan na Vanguard Tordue Salem.

Kusan mako biyu kenan da dan jaridar ya yi batan dabo a Abuja, babban birnin kasar.

Ranar Litinin yan jarida karkashin kungiyar NUJ sun gudanar da zanga-zanga a hedikwatar ‘yan sanda a Abuja, kan abin da suka kira ‘nuna rashin damuwa’ kan batan abokin aikinsu.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Najeriya Frank Mba, ya bai wa yan jaridar tabbacin yin duk iya yinsu wurin gano inda dan jaridar yake.

Kuma ya ce sun cafke mutum shida kan batun yayin da ake ci gaba da bincike,

Kafin batan Tordue Salem shi ke dauko wa jaridar Vanguard rahotanni daga majalisar dokoki, kuma rabon da a sa shi a ido, ko a ji daga gare shi tun ranar 13 ga watan Oktoba.

Labarai Makamanta