An Bindige ‘Yan Kasuwar Arewa 7 A Jihar Imo

Rahotanni daga Jihar Imo dake sashin Kudu maso gabashin Najeriya na bayyana cewar an shiga zaman dar-dar biyo bayan kisan da aka yi wa wasu ‘yan kasuwa su 7 daga yankin arewacin kasar.

Rahotanni sun ce an harbe mutanen ne a lokuta daban-daban a garin Orlu da Umaka da ke karamar hukumar Njaba tsakanin ranar Juma’a da Asabar.

Wani da abin ya faru a kan idonsa Harisu Umaru Ishiaku, ya ce wadanda suka yi kisan suna sanye ne da kayan sojoji, kuma da misalin karfe 8:30 na dare ne suka shiga kasuwar Afor Umuaka suka farwa mutanen.

Yace hudu daga cikin wadanda aka kashe da shekarunsu ke tsaknin 30 zuwa 45 sun dade suna rayuwa a yankin na shekaru masu yawa.

Hakan yasa ya yi zargin maharan baki ne, domin kuwa a cewarsa ba a taba samun wata matsala ba tsakanin wadanda aka kashe da kuma al’umar Umuaka.

kamar yadda shugaban ‘yan kasuwa Hausawa na Imo Mallam Ibrahim Abdulkaddir ya bayyana cewa, harin farko ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da wasu masu sayar da nama ke kokarin tashi.

Kawai sai ga wasu mutane a mota kirar Sienna suka bude musu wuta.

Ya ce a koma yanayi mai kama da juna aka kashe wasu ‘yan kasuwa a Umuaka.

Abdulkadir ya ce mafi yawan ‘yan kasuwar Hausawa da ke Orlu yanzu suna rayuwa ne cikin firgici, wasunsu ma sun gudu sun koma Owerri.

Labarai Makamanta