An Bankado Kazamar Cuwa-Cuwa A Shirin Ciyar Da Dalibai

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a wani sabon magudi da aka bankado a aikin ma’aikatar jinkai da jin dadin al’umma, gwamnatin tarayya ta bankado makarantun karya 349 a jihar Nasarawa.

Kwamitin tattara bayanai na shirin ciyar da daliban makarantu na gwamnatin tarayya ce ta bankado wannan almundahanan. Mallam Abdullahi Usman, wanda shine shugaban kwamitin kuma mai baiwa ministar jinkai Hajiya Sadiya Umar shawara ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai wajen gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.

A cewarsa, wasu jami’an ma’aikatar ke cinye kudaden ciyar da dalibai a jihar. Yace a farko, an shirya ciyar da makarantun gwamnati 1203 a fadin jihar.

A cewarsa: “Bayan bincike, kwamitin ya gano cewa makarantu 349 na karya ne babu su, yayinda wasu jami’ai ke zuba kudaden a aljihansu na ciyar da dalibai.” Ya kara da cewa wasu manya a ma’aikatar daga Abuja sun yi kira ga a cire jihar Nasarawa daga shirin gaba daya saboda wannan abinda ya faru.

Amma ba’a amince da hakan ba saboda ‘yayan talaka ne zasu rasa. Ya ce tuni an sallami shugaban shirin na jihar da jami’in da aka baiwa hakkin ayyukan.

Labarai Makamanta