An Bankado Kazamar Badakala A Babbar Kotun Bauchi

Daga Adamu Shehu Bauchi

Awani mataki na dakile ayyukan ma’aikatan kotu Yan’damfarar da suka jima suna cin karen su babu babbaka a babban Kotun Jihar Bauchi ta wajen bayar da rasitai na boge domin azurta kawunan su, Babban Kotun ta fitarda sabbin tsare tsare na hidimar tsaro irin na zamani, wanda za’abawa duk wanda yazu neman wani abu da ya shafi bayar da takarar shaida na rasit

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin Babban Hadimin Kotun wato (Chief Registrar) lauya Emmanuel Dan’juma Sublim. am lokacin da yake zan’tawa da manema labarai a ofishinsa

Babban Lauyan Sublim, yayi gargadi kan wan nan mummunar dabi’a da wasu ma’aikatan Kotun suke aikatawa, tare da jam kunne mutane da kamfanoni masu zaman kansu, da suyi hattara a duk lokacin da suka sami kansu a Kotun, kana yace, sa’anna kuma su amince da wan nan sabon tsari don amfani kansu da ita kanta babban kotun.

“Ayyukan irin wadan nan mutane da suke bada takardun shaida Kamar su (Affidavits) da sauran takaddunnshaidar mallakan wani abu, Kotu yanzu ta bamu daman mu fitar da sabon tsari mai inganci da zai dakile aikata hakan”

Ya sake cewa, “wadan nan mutane sun kware wajen satar yakaddun shaida da Kan Sarki iron na kotu, suna karakaina a farfajiyar Kotun, suna farautar duk mutumin da ya shigo kotu don yin wadansu takaddu na shaida, su Kuma su fanfare shi nan take, wasunsu ma’aikatanmu me na kotu, wadansu kuwa ana hada baki dasu ne su rika yin wan nan mummunan dabi’a”, ya jaddada.

Sublim, ya ci gaba da cewa, “abun mamaki shine kudin da suke karba yafi na asalin wanda Kotun take karba a hannun mutane don karbar wata takardan shaida, kowace iri ce kuwa” yace sabon tsari zaiyi wahala a kwaikwayi irin shi na babban Kotun a yanzu.

Hadimin ya kirayi, wanda alhakin rantsuwar take kansa a kotun da ya sanya idanu sosai akan aikata hakan da kuma bin diddigin wan nan dabi’a.

Lauya Sublim, ya kara da cewa kotun ta shiga aikin wayar da kan al’umman da kamfanoni masu zaman kansu a cikin gari da kewaye,Kan Sabon tsarin na tabbatar da sahihancin takadun shaidar a duk inda aka gansu

Yace, “muna amfani da kafafen watsa labarai na Radio da Talabijin da kafar sada zumunta don fadakar da mutane baki daya”.

Labarai Makamanta