An Bankado Badakalar Kudade A Kungiyar Bercelona

Wani rahoto kan yadda aka gudanar da hada-hadar kuɗaɗe a ƙungiyar kwallon kafa ta Barcelona ya nuna cewa an aikata manyan laifuka da suka saɓa doka.

An yanke shawarar gudanar da binciken ne a watan Oktoban bara bayan gano cewa ana bin kungiyar bashin sama da dala biliyan ɗaya da rabi.

Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce kulob din ya kai koke makon da ya wuce ga masu shigar da kara na cikin gida don ya gano an aikata ba daidai ba a lokacin mulkin Josep Maria Bartomeo da ya gada.

Labarai Makamanta