An Bada Umarnin Kamo Tsagerun Da Suka Kaiwa ‘Yan Sanda Hari A Imo

Babban Baturen ‘Yan sandan Najeriya Sufeta Janar Mohammed Adamu, ya dora alhakin kai hari ofishin yan sanda na jihar Imo akan kan kungiyar Tsagerun Inyamurai (IPOB) inda ya bayyana fusatarshi akan haka da kuma ɗaukar matakan da suka dace wajen ladabtar da Tsagerun.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sanda, CP Frank Mba ya fitar a madadin sufeta janar na ‘yan sandan, ya ce Shugaban ‘yan Sandan ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo ya gudanar da sahihin bincike da nufin gano wadanda suka kai harin domin su fuskanci abinda doka ta tanadar a kansu.

Ya kuma bada umurnin aikewa da ‘yan sanda na musamman zuwa Imo domin karfafa tsaro a jihar. “Sufeta Janar na Yan sanda, Adamu, ya bada umurnin tura karin ‘yan sanda na PMF da sauran yan sanda na musamman zuwa Jihar Imo don inganta tsaro a jihar.

Shugaban ‘Yan Sandan ya bada wannan umurnin ne bayan harin da aka kai wa jami’an tsaro ciki har da hedkwatar yan sanda na jihar Imo da Hedkwatar Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali, NCS, a Owerri a safiyar ranar Litinin 5 ga watan Afrilun 2021.

“Binciken da aka fara yi ya nuna cewa maharan da suka iso masu yawa dauke da mugan makamai kamar GPMG, AK49, RPGs, da bamabamai na IED, mambobin kungiyar masu neman kafa kasar Biafra ne wato IPOB da Eastern Security Network, ESN, ” a cewar sanarwar .

Sanarwar ta ce ‘yan sandan da ke aiki sun dakile yunkurin da aka kai na nufin shiga wurin ajiye makamansu domin a sace. Kazalika, babu wani dan sanda da ya rasa ransa illa guda daya da ya samu raunin bindiga a kafadarsa.

Bayan Allah-wadai da harin IGP ya bada umurnin tura karin jami’ai domin kare afkuwar hakan a gaba da kuma kare kai hari a wasu yankunan jihar.

Ya ce an kwato daya daga cikin motocin da maharan suka kai harin da shi kuma ana bincike a kansa. Muhammad Adamu ya ce rundunar tana iya kokarinta don dakile ayyukan bata gari da ke neman kawo wa hadin kan kasar nan cikas da zaman lafiyan yan Nijeriya.

Labarai Makamanta