An Ƙaddamar Da Takarar Saraki A Mahaifar Buhari

Rahotanni daga birnin Daura Mahaifar Shugaban kasa Buhari dake Jihar Katsina na bayyana cewar wasu matasa a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar ‘Not Too Young To Run’ da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam’iyyar PDP da sauransu.

“Mun yanke shawarar cewa za mu goyi bayan wanda ke son cigaban matasa kuma Sanata Saraki ne kadai ya cika wannan ka’idar. “Dukkanmu mun san rawar da ya taka don ganin an aiwatar da dokar Not Too Young To Run a Majalisar Tarayya a lokacin yana shugaban majalisa.

“Mun kuma san cewa shine kadai mamba na kwamitin zartarwa na kasa na PDP daya dage cewa dole jam’iyyar ta tallafawa matasa sannan ya goyi bayan matasa su iya yin takara a jam’iyyar,” in ji shi.

Hon Adam ya kuma ce tsohon gwamnan na jihar Kwara ya dauki nauyin dubban matasa domin su kara karatu a jami’o’i daban-daban a duniya. Kazalika, shugaban kungiyar ya ce sun zabi kaddamar da kungiyar a Daura ne saboda nan ne karamar hukumar Shugaban kasa Buhari kuma domin su nuna wa duniya rashin gamsuwarsu da halin da kasar ke ciki yanzu.

Labarai Makamanta