Amurka Za Ta Dawo Wa Najeriya Dala Miliyan 23 Da Abacha Ya Kai Ajiya

Gwamnatin Najeriya da Amurka sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar maido da dala miliyan 23 da ake zargin Abacha ya wawure zuwa gida Najeriya.

Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Leonard ce ta sanya hannu a madadin gwamnatin Amurka yayin da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin kasar Abubakar Malami ya rattaba hannu.

A nasa jawabin, Malami ya ce matakin mayar da kudaden, ya samo asali ne daga wasu jerin tattaunawa da tarukan da aka yi tsakanin Najeriya da ma’aikatar shari’a ta Amurka da kuma hukumar yaki da laifuka ta kasar Birtaniya.

Babban lauyan ya ce kudaden za a yi amfani da su ne wajen kammala aikin titin Abuja zuwa Kano da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da kuma gadar Neja ta biyu.

Da take jawabi a wajen rattaba hannun, jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Leonard ta ce, “Ma’aikatar shari’a ta Amurka da hukumar FBI sun kwace wadannan kudade ne a matsayin mayar da martani ga Janar Abacha da mukarrabansa da suka keta dokokin Amurka a lokacin da suka wawure wadannan kadarorin ga Amurka da kuma wasu kudade a asusun a Birtaniya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply