Amurka Ta Cire Najeriya A Jerin Kasashen Dake Tauye ‘Yancin Addini

Rahoton dake shigo mana daga Birnin Washington DC na Amurka na bayyana cewar Kasar ta Amurka ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da ta ce suna tauye ‘yancin masu yin addini a kasashensu.

Amurkan ta saka China, Rasha da wasu kasashe takwas a jerin kasashen da ta ce suna amfani da karfin iko wurin tauye hakkokin masu addini.

Sakataren Amurka Antony Blinken ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar mai taken ‘Religious Freedom Designations’.

A shekarar 2020 ne Amurka ta saka Najeriya da wasu kasashe shida a jerin kasashen da ke tauye hakkin masu addini ko kuma rashin daukan matakan kare masu addinin.

Amma an cire Nigeria cikin jerin kasashen da aka fitar a shekarar 2021. Blinken, wanda a yanzu yana kasar Kenya da ke Gabashin Afirka don ziyarar aiki, zai karaso Najeriya a wannan makon don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari da wasu manyan jami’an.

Sakataren na Amurka, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba ya ce: “Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin ta na kare hakkin masu addini a kowanne kasa.” Blinken ya ce gwamnatin Amurka za ta cigaba da saka takunkumi kan kasashe da gwamnatocin da ke hana ‘yan kasarsu ‘yancin yin addinin da suke so.

Kasashen da Amurka ta lissafa a matsayin masu tauye ‘yan cin addini sun ne:

1. Burma

2. China

3. Eritrea

4. Iran

5. DPRK

6. Pakistan

7. Rasha

8. Saudi Arabia

9. Tajikistan

10. Turkmenistan

Labarai Makamanta