Amurka Ta Bayyana Matsayarta Game Da Najeriya

Rahotanni daga birnin Washington DC na kasar A Amurka na bayyana cewar a ranar Talata, Sakataren ƙasar Amurka, Antony J. Blinken, ya ziyarci Najeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually) inda ya gana da shugaba Buhari da kuma ministan kasashen waje, Geoffrey Onyeama.

Mutanen uku sun tattauna akan abubuwa da dama, waɗanda suka haɗa da; yadda zasu haɗa kai wajen yaƙar ta’addanci da rashin tsaro, gyaran ɓangaren lafiya, bunƙasa tattalin arziƙi da sauransu.

Hakanan kuma shugaba Buhari ya tattauna da sakataren kan yadda za’a bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasar Amurka da Najeriya, domin cimma biyan bukatun muradun karni a Najeriya.

Bayan wannan tattaunawar ne gwamnatin ƙasar Amurka ta fidda bayani kan alaƙar dake tsakanin ƙasashen biyu. A bayanin data fitar gwamnatin tace: “Ƙasar data fi kowacce ƙasa yawan jama’a, damokaradiyya, da kuma tattalin arziƙi a nahiyar Africa ita ce Najeriya, Najeriya tana ɗaya daga cikin abokan mu masu muhimmanci a duniya.”

“Kasancewar shekarar 2020 tazo da ƙalubale da yawa kuma ta aje tarihi, Najeriya ta fusaknci ƙalubale da yawa a yayin da Ƙasar ke bikin cika shekaru 60 da samun yancin kai.” “Najeriya ita ce ƙasar da aka fi samun mutanen dake zuwa ƙasar Amurka daga Nahiyar Africa, inda akwai ‘yan asalin Najeriya 500,000 dake zaune a ƙasar Amurka.”

Labarai Makamanta