Amnesty Ta Yi Kiran A Gaggauta Sakin Dalibin Da Ya Soki Aisha Buhari

Kungiyar Kare Hakkin Dan’adam ta Amnesty International ta yi kira da a gaggauta sakin Aminu Adamu Muhammed, dalibi dan shekara 23 a Jami’ar Tarayya ta Dutse, wanda jami’an tsaro da ake zargin jami’an DSS ne su ka kama tun a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2022 da tsakar dare, kan wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, da ake zargin cin mutunci ne ga uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari.

A ranar 8 ga watan Yuni ne Muhammad ya wallafa hoton Aisha Buhari a shafinsa na twitter, inda ta yi kiba a hoton, sai ya rubuta a saman hoton cewa fito kitso tare da taken: “Mama ta ci kudin talakawa ta koshi”.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Amnesty International ta aikewa DAILY NIGERIAN, ta yi kakkausar suka kan kamun da aka yi wa Aminu, inda ta ce ‘yan uwa da abokan arziki sun yi zargin cewa an tsare shi ne ba tare da sanin inda ya ke ba, tare da yi masa mugun duka, gallazawa da sauran nau’ukan azaba.

“Tun da aka kama shi babu wanda ya iya ganinsa tsakanin iyalansa ko lauyoyinsa.

“Akwai zato mai karfi cewa jami’an tsaron Najeriya na tsare da Aminu a wani wuri da ba a san ko ina ba ne a Abuja.

Sanarwar ta ce “Amnesty International ta yi kira ga hukumomi da su sake shi daga tsare shi ba bisa ka’ida ba, tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda ake zargi da azabtarwa da kuma wasu laifukan da ake yi masa.”

Labarai Makamanta