Amfani Da Tsoffin Kudi: Gwamnatin Tarayya Ta Kalubalanci Hukuncin Kotu

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kotun kolin Najeriya tayi watsi da karar da gwamnonin APC suka shiga ne bukatar soke ranar 10 ga Febrairu, 2023 matsayin ranar karshe na daina amfani da tsaffin takardun Naira.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kotun koli ba tada hurumin sauraron karar da gwamnonin suka kai.

Gwamnonin da suka shigar da kara sune gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i, Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello. Gwamnonin su uku sun gabatar da bukata gaban kotun koli na a hana shirin haramta amfani da tsaffin takardun Naira na N1000, N500 da N200 da gwamnatin tarayya da babban bankin tarayya CBN ke kokarin yi a ranar 10 ga Febrairu.

Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami, wanda ya mayar da martani kan karar ya ce wannan lamari ba tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi bane, wannan lamarin shiri ne na CBN kawai. Ya ce saboda haka wannan kara bata cancanci a kaita kai tsaye wajen kotun koli ba.

Ya ce babban kotun tarayya ya kamata a fara kai tukunna. Saboda haka Abubakar Malami ya bukaci kotun koli ta soke hukuncin da tayi ranar Laraba.

Labarai Makamanta